Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar White House Ta Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Rasha Da Taliban


Jagororin ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar dokokin Amurka, sun yi ca akan Fadar gwamnatin Amurka ta White House inda har daya daga cikin su ya zargi shugaban kasar da wasu hadimansa da kokarin yaudarar Amurkawa don su yarda da cewa zargin da ake yi Rasha na biyan kudi ana kashe dakarun Amurka da na hadin gwiwa a Afghanistan ba gaskiya ba ne.

Sukar wacce ta fito daga bakin shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi ta biyo bayan wani zaman sauraren bahasi da darektocin hukumar leken asiri da na hukumar tsaron kasa suka yi tare da sabon darektan hukumar tattara bayanan sirri da aka nada a kwanan nan.

Duk da cewa Pelosi ta ki ta ce uffan kan bayanan sirrin, amma ta ce yunkurin da Shugaba Donald Trump da hadimansa suke yi na yayyafawa batun ruwa, tamkar cin amanar dakarun Amurka da ke yankin ne.

Manyan jami’an White House ciki har da mai ba da shawara kan harkar tsaro Robert O’Brien, sun yi ta kare matakin da aka dauka na cewa kada a sanar da shugaba Trump zargin da ake yi cewa Rasha na biyan mayaka da ke samun goyon bayan Taliban, don su rika kashe dakarun Amurka da takwarorinsu na hadin gwiwa a Afghanistan.

Ita dai Rasha da kungiyar ta Taliban sun musanta wannan zargi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG