Accessibility links

Fadar White House Za Ta Yi Maganin Tsattsauran Ra'ayin Cikin Gida

  • Halima Djimrao-Kane

Fadar White House ko Maison Blanche ta shugaban kasar Amurka

Manufar shirin, ita ce, bayar da babban fifiko da kara maida hankali ga yaki da mummunan tsattsauran ra’ayi da ta’addanci salon na al-Qaida

Gwamnatin shugaba Barack Obama ta gabatar da wani shirin yaki da mummunan tsattsauran ra’ayi na cikin gida.

Shirin mai shafuka 20 wanda aka gabatar a jiya Alhamis, yayi dalla-dalla game da daukan wasu matakai na takamaimai da nufin karfafa mu’amala da fadada ta, a unguwannin dake iya fadawa cikin sharrin masu mummunan tsattsauran ra’ayi.

Manufar shirin, ita ce, bayar da babban fifiko da kara maida hankali ga yaki da mummunan tsattsauran ra’ayi da ta’addanci salon na al-Qaida, da sassan su da kuma masu sha’awar yin koyi da su. Haka kuma an yi nunin cewa shirin ba zai bar sauran ayyukan tsattsauran ra’ayi ba, har aka yi musali da hare-haren da wani baturen kasar Norway mai tsananin tsattsauran ra’ayi ya kai a cikin watan yuli.Kuma a cikin shirin an ce kasashe masu 'yancin walwala da sakewa na fuskantar barazana daga dimbin masu mummunan tsattsauran ra'ayi iri-iri.

Shirin ya bukaci daukan sabbin matakan kwalailaice irin rawar da intanet da kuma sauran kafofin sadarwa da musanyar ra'ayi ta intanet ke takawa wajen maida Amurkawa masu tsananin tsattsauran ra'ayi daga kasashen waje. Haka kuma shirin ya bayar da jerin matakan da za a iya dauka a gano unguwannin da masu mummunan tsattsauran ra'ayi ke iya zuwa neman mabiya da kuma maida jama'a masu tsananin ra'ayi, don a hada su da ayyukan yaki da ta'addancin da gwamnatin tarayya da jahohi da kuma kananan hukumomi ke gudanarwa.

An kafawa sabon shirin wata rundunar musamman ta gogaggun jami’an tsaro daga ma’aikatu daban-daban domin a tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta na hulda ta kut da kut da jama’ar kasa. Kuma an tsara cewa shekara-shekara rundunar jami’an tsaro za ta rika yiwa shugaban kasa bayani akan aikin da ta gudanar.

XS
SM
MD
LG