Fafaroma Francis na ci gaba da murmurewa daga cutar pneuomonia bayan da sakamakon hoton kirjinsa da aka dauka ya nuna yana samun sauki.
A farkon wannan mako, likitoci sun ce rayuwarsa ba ta cikin hadari
Sabon rahoton likitoci ya bayyana cewa yanayin Fafaroma mai shekara 88 yana daidaita, amma an lura cewa yana fama da rashin karfin jiki.
A ranar Alhamis, Francis zai cika shekaru 12 da zabensa a matsayin Fafaroma na 266.
Fadar Vatican ba ta bayyana yadda za a yi bikin wannan rana ba.
A ranar Juma’a mai zuwa, Fafaroma Francis zai cika makonni hudu yana jinya a asibiti.
Dandalin Mu Tattauna