Accessibility links

Fafaroma Ya Gayawa Shugaban Rasha Putin Ya Tabbatar da Zaman Lafiya a Ukraine


Fafaroma Francis da Shugaban Rasha Vladimir Putin

Yayin da shugaba Vladimir Putin ya zayarci fadar Fafaroma, Fafaroma Francis ya fada masa ya tabbatar da zaman lafiya a Ukraine, yakin da yaki ya daidaita

Fafaroma Francis ya yi kira ga shugaba Vladimir Putin da ya ziyarceshi ya kuma yi yunkuri na zahiri dangane da wanzar da zaman lafiya a gabashin Ukraine da yaki ya daidaita.

Sanarwar da fadar Vatican ta fitar jiya Laraba bayan ganawar sa’a daya tsakanin Fafaroma da Putin tace, Fafaroman ya jadada cewa, tilas ne a yi kokari sosai wajen kawo karshen tawayen da ‘yan aware masu samun goyon bayan Rasha suka fara watanni goma sha hudu da suka shige. Kimanin mutane dubu shida da dari biyar suka mutu tunda aka fara fadan.

Sanarwar ta kuma ce, shugabannin biyu sun amince da muhimmancin samar da yanayin tattaunawa, kuma dukan bangarorin biyu su kiyaye yarjejeniyar Minsk daaka sawa hannu a watan Fabrairu tsakanin Rasha, da Ukraine da Faransa da kuma Jamus. Masu kula da lamura na kasa da kasa sun ce ana yawan keta yarjejeniyar.

Rasha ta sha musanta zargin kasasahen turai cewa, tana tanadawa ‘yan aware makamai da kuma tura dakarun Rasha kan iyaka domin yaki. Ta jadada cewa, mayakan Rashan da aka gani ko kuma aka kama a gabashin kasar dake Magana da Rashanci masu aikin sa kai ne.

XS
SM
MD
LG