Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabargazar Lalata: Fafaroma Ya Ki Amincewa Da Murabus Din Babban Fada Na Faransa


Yanzu haka an yanke wa babban limamin Cocin Katolika na Faransa hukuncin daurin watannin shida, saboda kin sanar da hukumomi laifin lalata da wani Firist ya aikata.

Fafaroma Francis, a jiya Talata, ya ki amincewa da murabus din da Cardinal din Faransa Philipe Barbarin ya yi, bayan an same shi da laifin rashin sanar da ‘yan sanda wasu zarge-zargen aikata lalata, ta wajen amfani da isa.

Jiya Talata Barbarin ya ce ya mika takardar yin murabus dinsa ga Fadar Vatican, to amma kuma Fafaroma, a ta bakinsa, “Ya kawo batun yin kyakkyawan zato ga wanda ake zargi, don haka bai rattaba hannu a kai ba.”

A maimakon haka, Fafaroma Francis ya bukaci Barbarin, wanda shi ne Fada na kasar Faransa mafi girma da tabargazar lalata da yara kanana, wadda ta dabaibaye majami’ar Katolika a fadin duniya ta shafa, da ya yi abin da ya ga shi ne mafi dacewa ga archdiocese din Lyon da ya ke Shugabanta.

Don haka Cardinal din mai shekaru 68, ya yanke shawarar zuwa hutu, saboda ya ji da wannan abin da ke gabansa, ya bukaci mataimakinsa da ya jagoranci archdiocese din.

An zartas ma Barbarin hukuncin daurin watanni 6, wanda ba za a aiwatar nan take ba, saboda rashin sanar da hukumomi laifin lalata da wani Firist ya aikata.

Firist din mai suna Benard Preynat, ana zargin ya yi lalatar luwadi da yara maza daga 1980 zuwa 1990.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG