Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faisal Maina Ya Tsere Zuwa Amurka-EFCC


Faisal Maina

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta ce Faisal Maina, dan tsohon shugaban hukumar garanbawul ga harkokin fansho Abdulrasheed Maina, ya keta sharudan belinsa ya tsere zuwa Amurka.

Babban lauya mai shigar da kara na hukumar EFCC Mohammed Abubakar wanda ya ya bayyana haka a babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, yace Faisal Maina da ake tuhuma da aikata laifuka uku da suka jibinci halallata kudin haram, ya gudu zuwa Amurka ne daga Jamhuriyar Nijar.

Alkalin da ke sauraron karar Faisal ya umarci a kwace kaddarorin da dan majalisar wakilai Sani Dan-Galadima, ya gabatar a kotu lokacin da ya tsaya wa Faisal da yake neman beli. Dan majalisar ya amince ya ajiye Naira miliyan 60 da kotu ta bukata daga duk wanda ya amince zai tsayawa Faisal kafin a bada belinshi.

Koto tana kuma tuhumar mahaifin Faisal Abdulrasheed Maina da aikata laifuka 12 da suka danganci halarta kudaden haram.

Kamar dansa Faisal, Sau biyu Abdulrasheed Maina yana tserewa bayan da aka ba da belinsa. Ko a shekarar da ta gabata, sai da mahaifin Fascal Abdulrasheed Maina, ya tsere zuwa jamhuriyar Nijar da niyar kaucewa fuskantar hukumci, kafin hukumar EFCC ta tasa keyarshi zuwa Najeriya inda aka tsaurara matakan ganin bai sake arcewa ba.

yan-sanda-sun-mayar-da-abdulrasheed-maina-najeriya

kotu-ta-sa-a-rufe-abdulrasheed-maina-a-gidan-yari

yadda-abdulrasheed-maina-ya-yanke-jiki-ya-fadi-a-kotu

Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina

Abdulrasheed maina na fuskantar shari'ar da ke zarginsa da wawure kudaden ‘yan fansho lokacin da ya jagoranci wani kwamitin aiki da cikawa na shugaban kasa kan fansho.

A lokutan baya, wata Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a tsare Sanata Ali Ndume wanda ya tsayawa Abdulrasheed maina, saboda ya gaza gabatar da tsohon shugaban tsohuwar hukumar kula da fansho ta Najeriya lokacin da ya tsallake beli ya fice daga Najeriya.

kotu-ta-gindayawa-ali-ndume-sharuddan-beli

kotu-ta-yi-watsi-da-dalilan-da-ndume-ya-bayar-na-neman-beli

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG