Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ban Ga Sammacin Kotu Ba Akan a Tsare Ni - Ali Ndume


ABUJA: Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa Ali Ndume

Sanata Ali Ndume ya ce Kotu ba ta bashi damar ya kare kansa ba bayan da ta bada umurnin a tsare shi a gidan yari.

Wata Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a tsare Sanata Ali Ndume a gidan yarin da ke Kuje saboda ya gaza gabatar da tsohon shugaban tsohuwar hukumar kula da fansho ta Najeriya, Abdulrasheed Maina.

Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta kudu, shi ne ya tsaya wa Maina wajen bada belinsa. Maina dai na fuskantar shari’a ne akan zargin halatta kudaden haram.

Duk da haka, Maina ya sha kin gurfana gaban Kotu domin ci gaban shari'ar.

Ali Ndume ya ce ya bukaci Kotun ta bashi dama ya kare kansu amma alkalin ya ce babu damar hakan tunda Maina bai bayyana gabanta ba kuma har an riga an bada umurnin a tsare shi, duk da cewa bai ga sammacin kamen ba.
Za ku ji bayanin halin da ake ciki nan gaba.

XS
SM
MD
LG