Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falesdinawa 15 Ne Suka Mutu Sakamakon Zanga-Zangar Da Suka Gudanar


An kashe Falesdinawa su 15 lokacin da suke zanga-zanga a bakin iyakar Izraela da Gaza

Maaikatar kiwon lafiya na Falesdinu ya ruwaito cewa mutane 15 ne suka mutu kana wasu daruruwa sun samu rauni a jiya jumaa, sakamakon jamiaan tsaron Israela da suka farmusu akan bakin iyakar Israela da Gaza.

Sojojin Israela suka ce sunyi anfani ne da rundunar su na fatattakar masu zanga-zanga, domin ganin sun kwantar da zanga-zangar da Falesdinawan sukeyi, wanda shine irin sa mafi girma da suka taba gudanarwa a wannan bakin iyakan.

Rikici dai ya barke sailin da dubban Falesdinawa suka dunfari bakin iyakar, wannan yasa sojojin kasar Izraela yunkurowa domin su dakatar dasu domin ko falesdinawan sun dunfari bakin iyakar hadi jifa, tare da mirgina tayoyin da suka cinna ma wuta suna tura su suna gangara baki iyakan.

Haka kuma sojoji na Izraela sun zargi ‘yan taadda dake son suyi anfani da damar zanga-zangar domin sukai hari abinda sojojin Izraela suka ce ba zata yiwu ba.

Maaikatar kiwon lafiya na kasar Falesdinu tace sojojin Iszaela sun sunyi harbin cikin cincirondon taron ko bayan sun harba musu hayakin nan mai sa kwalla.Wanda hakan yayi dalilin mutuwar mutane 15 kana ya jima mutane kusan 1,400 ciki ko harda mutane da suka kai 750 da harbin yayi musu rauni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG