Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fannin Kare hakkin Dan Adam Na Bukatar Jajirtattun Mutane- Manzon Majalisar Dinkin Duniya


Majalisar Dinkin Duniya
Majalisar Dinkin Duniya

Masu sharhi da masana harkokin hakkin dan Adam na ganin ana samun karuwar take hakkokin bil’adama a Najeriya. 

Jim Kadan bayan jawabai a taron cika shekaru 75 da kaddamar da yarjejeniyar kula da hakkokin bil’adama na duniya wato Universal Declaration of Human Rights, masu ruwa da tsaki da suka hada da babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya kuma mai kula da ayyukan jinkai, Mathias Schmale, hukumar kula da hakokkin bil’adama a Najeriya, NHRC, jakadan kasar Brazil A Najeriya sun jadada mahimmancin zakulo jajirtattun mutane don aikin kula da hakokkokin al’ummar kasa.

A ranar talata, 5 ga watan Disamban nan ne yarjejeniyar kula da hakkokin bil’adama ta majalisar dinkin duniya ta cika shekaru 75 bayan amincewa da ita da gomman kasashe suka yi a shekarar 1948, saidai a yayin murnar zagayowar wannan muhimmiyar rana, masana sun ce akwai saura jan aiki a gaban Najeriya kasancewar munin da ake gani a fannin take hakkoki da cin zarafin mutane a kasar.

Jamila Sidi Sirajo, wata uwa ce da aka yi ta ciwa zarrafi da take hakokkinta a gidan aure lamarin da ya kaita ga neman mafita a gaban kuliya da ya ki ci ya ki cinyewa hakan yasa ta zama mai fafutukar ganin an kare yara da mata ‘yan uwanta, inda ta ce dole ne gwamnati ta tashi tsaye don rufe dukkan hanyoyin da baragurbin masu hannun da shuni ke bi wajen take hakokkin mutane don suna da hali.

Masu sharhi da masana harkokin hakkin dan Adam na ganin ana samun karuwar take hakokkin bil’adama a Najeriya.

Masu ruwa da tsaki a wajen taron sun jaddada, sakonnin da ya fito daga bakin babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya kuma mai kula da ayyukan jinkai, Mathias Schmale, na ya kamata a fahimci cewa bada muhimmanci ga zakulo jajirtattun mutane don daukar matakan da suka dace a aikin kamar yadda aka gani a kasar Brazil, yadda mutane masu ra’ayi mai karfi a fafutukar ganin sauyi suka jagoranci yaƙin kawar da bautar da mutane a Brazil din.

Schmale ya kuma ce har yanzu Nijeriya ba ta sami irin ci gaban da ake bukata a wajen kare hakkin bil’adama ba, duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar da dokoki, amma ana samun koma baya wajen aiwatarwa yana mai cewa abin da ake bukata a nan shine a samo jajirtattun mutane su yi jagorancin wannan muhimmin aikin kamar yadda aka gani a Brazil, Amurka da sauran kasashe don a yi nasara a gwagwarmayar.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar jihar Ondo ta kudu da yamma kuma shugaban kwamitin kula da hakokkin bil’adama na majalisar dokokin Najeriya, dakta Abiola Peter Makinde, ya ce aikin kwamitin da yake jagoranta shi ne kula da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasar don tabbatar da cewa ana aiwatar da dokokin Najeriya a fannin kuma zai tabbatar da cewa ya bi kadun aikin yadda ya kamata don gano inda matsalar take domin a samo mafita mai dorewa.

A yayin bikin cika shekaru 75 da kafa Yarjejeniyar kare Haƙƙin Bil Adama ta Duniya a Najeriya jakadan kasar Brazil a Najeriya, Ambassada Joao Marcelo Soares wanda shi ne mai masaukin baki ya ce yawancin ƙasashen duniya na fama da matsalolin take haƙƙin bil’adama kuma yanzu aikin shi ne a hada karfi da Karfe wajen rage ko kawo karshen matsalolin.

A nata bangaren, mataimakiyar darakta a hukumar kare hakkin Bil’adama, Fatima Agwai Muhammad, ta ce sakon su ga yan Najeriya shi ne su tsare hakkokinsu da na ‘yan uwansu.

Yarjejeniyar kula da Haƙƙin dan adam ta Duniya wata muhimmiyar takarda ce a tarihi wadda wakilai masu mabanbantan ra’ayoyi da al’adu daga kowane yanki na duniya suka tsara kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana sanarwar hakan a ranar 10 ga Disamban shekarar 1948 inda ƙuduri na 217 sakin sashi na A ya kasance a matsayin ma'auni na gama gari na dukkan al'ummomi da sauran jama’ar duniya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG