Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa, Jamus Da Amurka Sun Goyi Bayan Matakan Da Birtaniya Ta Dauka Kan Rasha


Firayim Ministar Birtaniya Theresa May
Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

Bayan Birtaniya ta zargi Rasha da yin anfani da guba wajen hallaka wani dan asalin Rasha din tsohon mai leken asiri da diyarsa, ta kori jami'an diflomasiyar Rasha 23 kuma kasashen Faransa da Jamus da Amurka sun goyi bayan matakin ladaftar da Rasha

A Wuri daya kuma Shugabannin kasashen Birtaniya,Faransa,Germany da Amurka gaba dayan su sunyi tir da guban da kasar ta Rasha tasa ma wani tsohon mai leken asiri dan kasar ta Rasha dake zaune a Birtaniya.,

Shuganannin sun kira wannan babban laifi ne anfani da wannan sinadarin mai guba a kasar Turai domin ko rabon da ayi anfani da irinsa tun lokacin yakin duniya na biyu.

A cikin wata sanarwan hadin gwiwa da suka fitar jiya Alhamis Prime Ministan Birtaniya Theresa May,Shugaba Emanuel Macron na Faransa, Angella Merkel da Shugaba Donald Trump sunce ba wani bayani da kasar na Rasha zata yi da zai zama karbabbe cewa wai ba ita ce ta aikata wannan danyen aikin ba.

“Sukace muna kira ga kasar ta Rasha data amsa duk wata tambayar da aka yi mata dake da nasaba da wannan harin”

Sai dai Rasha ta musunta wannan zargin

Ana saran Prime Ministan Birtaniya May nan bada jimawa ba ta bayyana matakai da Birtaniya zata dauka akan Rasha game da wannan, wanda ya hada da korar jami’an jakadancii Rasha har su 23 wanda wannan shine abinda aka jima da ganin irin sa tun a shekarar 1971 lokacin yakin cacan baki.

Sai dai ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov yace haka ita Moscow zata kori jami’an jakadancin Birtani a kasar nan bada jimawa domin ramuwar gayya.

Lavrov ya bayyana wannan matakin da May ta dauka a matsayin shirme, yace tayi haka ne da niyyar dauke hankalin kasar na Birtaniya dake fama da matsalar fita cikin kungiyar tarayyar turai

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG