Accessibility links

Faransa Tace Ba Zata Fice Daga Mali Ba Sai Ta Kwato Kasar Daga Hannun Mayaka

  • Grace Alheri Abdu

laftanar kanar Frederic na Faransa (C) da kanar Seydou Sokoba na kasar Mali suna amsa tambayoyin 'yan jarida a Niono, January 20, 2013.
Ministan tsaron kasar Faransa Jean Yves Le Drian yace kasar ba zata daina daukar matakan soja a Mali ba har sai ta kwato dukkan yankunan kasar daga hannun ‘yan kishin Islama.

Le Drian ya shaidawa tashar talabijin ta kasar Faransa jiya Lahadi cewa dakarunsa ba zasu bar ko da taqi guda na kasar Mali a hannun ‘yan tawayen ba.

Dakarun kasar Faransa sun shiga kasar ta yammacin Afrika makon jiya bisa ga bukatar da gwamnatin kasar Mali ta gabaar. Mayakan kishin Islama masu alaka da kungiyar al-Qaida, da suka kwace ikon arewacin kasar bara, sun fara kutsawa kudu suka doshi Bamako babban birnin kasar.

Dakarun kasar Faransa sun taka masu birki, yanzu sun nufi arewa bayan gumurzun kwanaki da dama.

Laftanar kanar Emmnuel Dosseur na kasar Faransa yace dakarun suna kokarin hada hannu da sojojin da suka riga suka shiga garin Niono da Sevare.

Wakilin Muryar Amurka wanda yake Sevare a halin yanzu, ya bayyana garin a matsayin wanda yake cikin yanayi na yaki, inda dakarun Faransa da na kasar Mali suka mamaye, yayinda farin kaya suka kauracewa garin.

Garin Sevare yana da filin jirgin sama mai muhimmanci da zai iya zama sansanin wani aikin soja a arewacin kasar.
XS
SM
MD
LG