Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Man Fetur Na Ci Gaba da Tashi a Kasuwar Duniya


 Kungiyar OPEC
Kungiyar OPEC

Matakan da kasashen Kungiyar OPEC da Rasha da kawayenta suka dauka na takaita man da suke kaiwa kasuwa, yanzu za a ce kwaliya ta biya kudin sabulu saboda farashin man ya fara tashi a kasuwar duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa kawancen da kasashen OPEC da na Rasha suka yin akan takaita yawan man da zasu kai kasuwar duniya a wannan shekarar ta 2018 sun soma yin tasiri.

Farashin man fetur ya haura sama da $68 kowace gangar danyen mai a kasuwar duniya. Da alama hankan zai ci gaba da aukuwa nan da watanni uku masu zuwa saboda ana kyautata zaton kasashen turai zasu bukaci man fiye da shekarar da ta gabata.

Har wa yau kungiyar OPEC na ci gaba da kara rage man fiye da alkawarin da ta yi can baya lamarin da ya sa wasu kasashe irin su Amurka suka shiga yin anfani da ajiyar man da suke dashi. Kasar Amurka ce kasuwar mai da tafi girma a duniya kuma it ace ta fi kowace kasa aiwatar da kasuwancin man fetur a bayyane ba tare da wata muna muna ba a cewar Reuters.

Ajiyar mai a Amurka ya ragu da kimanin ganga miliyan hudu da dubu dari daya.

Duk da cewa wasu kasashen OPEC kamar Iran sun ce basu damu da karin farashin mai ba, kasashen da tattalin arzikinsu ya kusa durkushewa lokacin da farshin mai ya fadi warwas suna maraba marhaban da tashin farashin man da fatan zai dore (Reuters)

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG