Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Shiga Yanar Gizo Zai Ragu Da Kashi 65 A Najeriya


Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo (Twitter/ Laolu Akande)

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za'a rage farashin Data ta amfani da yanar gizo da kashi 65 cikin 100 da zarar an kammala aikin Shimfida Na’urori.

A daidai lokacin da matasa a Najeriya ke sa ido kan yadda kwamitin da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa domin dawo da aikin dandalin Tuwita a kasar, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyyana cewa gwamnati na wani gaggarumin aiki na tabbatar da rage farashin data domin shiga yanar gizo a kasar.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shirin zai rage farashin kowanne gigabait din data daya da kusan kashi 70 cikin 100, ta yadda farashin ba zai wuce naira 390 ba nan da shekara 3 masu zuwa.

Hakan kuwa in ji shi, na da manufar ba ‘yan kasar damar shiga yanar gizo a saukake, amma har sai an kammala aikin shimfida na'urori a fadin kasar.

Ya kara da cewa ko bayan rage farashi, shirin na shimfida na’uro’ri zai kuma kara saurin kafar intanet zuwa megabait 10 a kowanne dakika.

Mataimakin shugaban wanda ya samu wakilcin karamin ministan ma’aikatar ayyuka da gidaje, Abubakar D. Aliyu, ya bayyana hakan ne a yayin jawabin bude taron masana masu safiyo na gidaje da kadarori na Najeriya wato NIESV na kwanaki 6 karo na 51 a birnin tarayya Abuja.

Ya ce gwamnati za ta shigo da ma’aikatan safiyo wajen aikin shimfida na’urorin, musamman ta bangaren gine-gine.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar masana masu safiyon gidaje da kadarori na Najeriya, Emmanuel Okas, ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta tsame hannunta daga harkar gina gidaje ta bar wa kamfanoni masu zaman kansu kamar yadda ta yi a bangaren sadarwa.

Haka kuma, Emmanuel Okas, ya bayyana cewa, aikin gine-gine daya ne daga cikin gagaruman hanyoyin habaka tattalin arzikin kasa kuma shigowa da kamfanoni masu zaman kansu cikin aikin zai taimaka matuka.

Alkaluma daga kamfanonin sadarwa a Najeriya kama daga MTN, GLO, Airtel da dai sauransu sun yi nuni da cewa, a halin yanzu, ana sayar da gigabait daya na data tsakanin naira 1,000 zuwa 1,200, saidai idan aka kwatanta da wasu kasashe a nahiyar Afrika farashin na Najeriya ya fi rangwame.

A wani bangare kuwa, masani a kan harkar fasahohin zamani da intanet, Yusufudeen A. Yusuf, ya ce kalaman na mataimakin shugaban kasa kan rage farashin data abu ne mai kyau, kuma idan gwamnati ta mayar da hankali wajen sa ido a aikin aiwatarwa za‘a samu nasara hainun.

XS
SM
MD
LG