Accessibility links

Daga kasar Senegal Furofesa Boube Namaiwa ya fadi albarkacin bakinsa dangane da rayuwar Nelson Mandela

Abokiyar aiki Grace Alheri Abdu ta tuntubi Farfasa Boube Na Marwa kan abun da zai fada game da marigayi Nelson Mandela, tsohon shugaban Afirka Ta Kudu kuma bakin mutum na farko da ya taba zama shugaban kasar.

Ya ce Nelson Mandela mutum ne wanda ya sadakar da kansa domin 'yan Afirka Ta Kudu bakake da ma wasu mutanen da basu da tushe a kasar domin su ba turawa ba ne. Ya yiwa Afirka Ta Kudu da ma Afirka gaba daya da rasuwar wanda ya kira gwarzonmu ta'aziya. Ya ce dalilin da ya kirashi gwarzo a karni na ashirin tun haihuwar Annabi Isa ba za'a samu gwarzo kamarshi ba. Cikin karnin nan da ya wuce babu wani gwarzo kamanshi domin mutum ne wanda ya sadakar da kanshi.

Ya ce ya kamata shugabannin Afirka su yi koyi da Nelson Mandela. Ya ce mutum na iya zuwa gidan kaso ya fito kuma ya zama shugaban kasa yadda idan yana son ya yi wa'adi barkatai har iyakar rayuwarsa da ya yin to amma tun farko ya ce wa'adi daya zai yi. Bayan ya bar shugabanci ya bar harkar siyasa gaba daya amma ya koma gefe daya yana yakar cutar kanjamau yana ceton jama'a. Ya ce wannan ya isa duk 'yan Afirka Ta Kudu su fito su yi bakin ciki domin sun rasa uban gaske domin bai makalewa shugabanci ba. Ya sake sadakar da kansa wurin taimakon jama'a. Abun da Nelson Mandela ya sa gaba shi ne cigaban Afirka da zaman lafiya.

Tsakanin Nelson Mandla da wadanda suke gwagwarmaya yau babu kwatamci domin basu iya yin abun da ya yi ba. Duk wani kokarin kare hakin bil adama da suka ce suna yi basu iya yi yadda Nelson Mandela ya yi domin shi bai nemi arziki ba ko tara kayan duniya ba. To amma idan aka binciki masu kare hakin bil adama yanzu za'a samesu suna neman riba da suna ne. Ya ce a kasa kamar Afirka Ta Kudu da duk arzikin da take da shi da hulda da takeyi a duniya a ce ka yi wa'adi daya na shugabancin kasar a rokeka ka cigaba ka ki. Wannan irin hali na gari sai Nelson Mandela.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG