Accessibility links

Fashewar Bututun Iskar Gas cikin Birnin Abuja Ta Firgita Jama'a


Fashewar bututun iskar gas a Abuja
Sanadiyar irin hare-haren da kungiyar Boko Haram da wasu 'yan ta'ada suka sha kaiwa a wurare da dama a Najeriya har da babban birnin Abuja to kowane irin kara 'yan Najeriya suka ji musamman a arewa zasu firgita.

Fashewar bututun iskar gas a wani katafaren gini da yake da shaguna inda ake kasuwanci ta sa mutane a birnin Abuja sun firgita. Wani Alhaji Abubakar Alhasan Argungu dan kasuwa mazaunin Abuja wanda ya kwashe fiye da shekaru talatin yana tuka mota amma jin karar fashewar bututun ya sashi yin yunkurin juyawa baya da motarsa. Amma abun mamaki sabili da tsananin firgicewar da yayi ya kasa gane giyar sa motar yin baya.

Motocin kashe gobara sun sheka wurin da lamarin ya auku domin kashe wutar da take ta ci bal-bal yayin da 'yan yada jita-jita suna cigaba da cewa bam ne ya fashe. Yau Yakubu Yobe ya ji karar kuma ya hango wutar lokacin da ta tashi. Ya ce sai da ya ga harbawar wutar sama har sau goma. Yace akwai wani mai wanke huluna wanda lamarin ya rutsa da kayansa. Wai ya rasa akalla huluna dari biyar.

Wadanda suka fi tafka asara su ne 'yan sabon ofishin nakasassu masu goyon bayan shugaba Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo inda babban allonsu da suka kafa ya kone kurmus. Akilu Jugunu shugaban kungiyar yace Allah Ya taimakesu domin su guragu ne da makafi da wutar ta kawo kansu da sun yi asarar rayuka da dama. Yace akalla dubu dari da hamsin lamarin zai shafa.

Ga karin bayani.
XS
SM
MD
LG