Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasinjoji 163, 878 Suka Amfana Da Tallafin Sufurin Lokacin Hutu Na Tinubu - Alake.


Dr. Oladele Alake
Dr. Oladele Alake

Fasinjoji 163, 878 ne suka ci gajiyar wannan tallafin sufurin na lokacin bukuwan Kirsimeti da hutun karshen shekara na shugaban kasa a cikin kwanaki 10 na farkon shirin.

WASHINGTON, D. C. - An bayyana hakan ne a ranar Lahadin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ministan ma’adanai da ci gaban kasa wanda shine Shugaban kwamitin Ministoci, Dr. Oladele Alake.

A cewarsa, gwamnatin ta fahimci cewa, bisa al’ada, ‘yan Najeriya sun saba tafiya zuwa garuruwansu a karshen shekara, suna kuma hasashen cewa, halin matsi da ake fama da shi, da kuma karin kudin sufurida ake dangantawa da tsadar sufurin a karshen shekara na iya kawo cikas ga ‘yan kasa da dama.

Ya yi nuni da cewa, shirin sufuri na lokacin hutun Kirsimeti da karshen shekara zai cirewa dimbin ‘yan Najeriya kitse a wuta.

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

A ranar 19 ga watan Disamba, 2023, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani sabon shirin bayar da agajin sufuri wanda zai samar da sufuri kyauta a kan hanyoyin hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC da kuma tallafin kashi 50 na kudin sufurin fasinjojin da ke tafiya kan tituna 28 da motocin bas a karkashin inuwar kungiyar Masu Bus-bus na Najeriya, ALBON

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG