Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fifa Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Maradona


Tsohon shahararren dan wasan kwallon Kafa na kasar Argentina Diego Maradona, ya ce kasar Ingila ta yi wa kasar Colombia "fashi da makami" a wasan da suka buga zagaye na 16, ranar Talata 3/7/2018, a gasar cin kofin duniya.

A cewar Diego Maradona, bugun daga kai sai mai tsaron gida da alkalin wasan mai suna Mark Geiger, ya ba kasar Ingila, inda dan wasanta Harry Kane, ya cE bai dace a bataba.

Tum bayar da wannan fenaretin Kyaftin din ‘yan wasan Colombia Radamel Falcao, ya zargi alkalin wasa Mark Geiger, da nuna banbancin a wasan inda ya kira wannan lamarin"abin kunya" ne a ga reshi.

A yayin wasan an nuna Maradona, sanye da rigar kasar Colombia yana murna lokacin da Yerry Mina, dan wasan baya na kasar Colombia, ya farke kwallon da aka shasu a mintuna 93 na Karin lokaci wadda hakan ya mai da wasan 1-1 daga bisani aka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an shafe mintuna 120 ana gwabzawa, inda aka cire Colombia da ci 4-3 (penalties).

Sai dai a nata bangaren hukumar dake kula da wasan kwallon Kafa ta duniya (Fifa) ta ce maganganun da Diego Maradona, yayi gaba daya basu dace ba kuma wannan batu game da alkalin wasa ba haka bane.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG