Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: Al'umman Jihar Filato Sun Bukaci Gwamnati Ta Samo Masu Tsaro


Gwamna Jihar filato
Gwamna Jihar filato

Al’ummomin kauyen Tattara da sauran kauyukan da rikici ya daidaita a karamar hukumar Kokona a Jahar Nasarawa sun bukaci gwamnati ta samar musu da tsaro don su koma yankunansu su yi noma.

Kusan makwanni uku ke nan tun bayan da wani rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje, yayin da mutanen kauyukan da ke kewaye da garin na Tattara suka yi gudun hijira zuwa garin Garaku, shalkwatar karamar hukumar Kokona a Jahar Nasarawa.

Wani mai suna Musa Bala ya ce ya rasa ‘yan’uwansa, an kuma kone gidaje da dam,a amma jama’a na zaune ne cikin tsoro da fargaba, dalilin da ya sanya kenan ba su koma kauyukansu ba, gashi kuma damina ta kankama za su fara aikin gona.

Ardo Aliyu na karamar hukumar Kokona ya ce sun yi zaman sasantawa kuma da yardar Allah ba za'a sake samun rikici a yankin ba.

'Yan Gudun Hijira A Jihar Filato
'Yan Gudun Hijira A Jihar Filato

Komishinan yada labarai da al’adu da yawon shakatawa na jihar Nasarawa, Yakubu Muhammad Lawal ya ce gwamnati ta nada kwamiti da zai rika sasantawa tsakanin wadanda ke zaman doya da manja don samun zaman lafiya mai dorewa a Jahar.

Duk da kokari da gwamnati ke cewa tana yi wajen magance rashin tsaron, yankuna da dama a jihohi na fuskantar nau’u’ka daban-daban nakalubalen tsaro da ke bukatar agajin gaggawa da magancewa.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG