Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya 

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya
Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin tankar man fetur a mahadar hanyar Bauchi, dake nan cikin garin Jos.

PLATEAU, NIGERIA - A wata sanarwa daya aikewa manema labarai, kakakin rundunar, DSP Alfred Alabo ya ce gawarwakin mutane goma da suka kone kurmus, an ajiye a mutuware a asibitin kwararru na jihar Filato.

Sanarwar tace motoci uku da keke NAPEP biyu ne suka kone.

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya
Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya

Wasu da suka ga yadda hadarin ya auku sun shaida cewa motar dake dankare da man fetur ce ta kwace wa direban ta fadi a kan hanya dake da cinkoson mutane, wanda ya janyo rasa rayuka da jikkatan wadansu mutanen.

Bayan aukuwar hadarin ne matasa suka farma jami’an hukumar kiyaye hadura da ‘yan kwana-kwana da suka zo don yin agaji, bisa cewa basu kawo agaji a kan lokaci ba.

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya
Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya
Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya
Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya

Alhaji Danjuma Khalid, jami’in kungiyar Jama’atu Nasril Islam a jihar Filato ya ce sun kwashe gawarwaki guda goma ya kuma ja kunnen matasa su rika kai zuciya nesa don ba hukumomi sukunin gudanar da aikinsu lokacin da ake neman taimako na gaggawa.

Jami’in hukumar NEMA a shiyyar Arewa ta tsakiya, Nuruddeen Musa ya bukaci gwamnati ta dakatar da tankunan dakon maid daga ratsa cikin gari lokacin da jama’a ke zirga-zirga.

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya
Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya

Ana yawan samun haduran manyan motoci a cikin garin Jos musamman saboda hawa da gangara da garin ke dashi, yanayi da al’ummar garin ke fatar gwamnati zata samar musu da mafita.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

 Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG