Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: Al’ummar Jihar Na Kira Ga Gwamnati Da Ta Dauki Matakan Tsaro Don Baiwa Dalibai Damar Samun Ilimi.


Wata Makaranta A Ghana
Wata Makaranta A Ghana

Yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, jihohin dake makwabtaka da birnin sun fara daukan matakan tsare rayukan al’ummarsu.

Matakin da gwamnatin Jihar Nasarawa ta dauka na rufe makarantun sakandare da firamare a Jahar ya sanya al’ummar Jahar yin kira wa gwamnati kan ta dauki matakan tsaro don baiwa dalibai damar samun ilimi.

Rufe makarantun ya zo ne a dai-dai lokacin da dalibai ke rubuta jarrabawa ta kasa da zai basu guraben shiga manyan makarantu.

Wani dake zaune a kan iyakar Abuja, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa rufe makarantun zai shafi harkar ilimi a Najeriya.

Honarabul Hafsat Abdullahi, wata uwa daga Jihar Nasarawa, ta ce matakin da hukumomi suka dauka na sallamar yara daga makarantun ya yi dai-dai saboda sai da lafiya ilimin zai samu.

Shiko Alhaji Garba ‘Dan Malam daga garin Keffi a Jihar Nasarawa ya ce tun farko sakacin gwamnati ne ya kawo ga halin da al’umma ke ciki, don haka ya ce dole a dauki matakan gyara.

Komishiniyar Ilimi a Jihar Nasarawa, Hajiya Fati Jimeta Sabo ta ce gwamnatin jihar ta Nasarawa ta rufe makarantun ne don kariya kan lamarin rashin tsaro a Abuja dake makwabtaka da jihar.

A halin da ake ciki dai, daukacin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da jami’o’i da wassu manyan makarantun jihar zasu kasance a rufe har sai lamura sun daidaita.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG