Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato: An Yi Kira Ga Hukumomin Tsaro Su Dauki Matakan Kare Al’umma


Lava flowing from an eruption of a volcano destroys a house in the Cumbre Vieja national park at Los Llanos de Aridane, on the Canary Island of La Palma, Spain.<br /> &nbsp;

Al’umomin Fulani da na Birom dake karamar humar Barikin Ladi a jihar Filato, sun bukaci hukumomin tsaro da su dukufa wajen gudanar da aikinsu na tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

Wannan kiran dai ya biyo bayan kisa da ramuwar gayya da a ‘yan kwanakin bayan nan suka yawaita a yankin karamar hukumar Barikin Ladi.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah a Barikin Ladi, Abubakar Gambo, ya ce da yammacin ranar Juma’a ne wasu fulani dake dawowa daga kasuwar Kara, su biyar cikin mota wasu ‘yan binidga suka bude musu wuta, suka kwashe mutanen suka kunnawa mutarsu wuta.

Shi kuma shugaban kungiyar matasan Birom na kasa, yayi kuka ne ganin yadda mutane ba sa iya zuwa gonakinsu, saboda fargabar irin kashe-kashe da ake yi. Wanda hakan yasa an yi asarar rayukan kusan mutane 20 cikin mako biyun da suka gabata.

Kakakin rundunar tsaro ta STP a jihar Filato, Manjo Umar Adam, yayi kira ga mutanen karkara da kar su ci gaba da daukar mataki a hannunsu, a nemi jami’an tsaro a yi musu bayani domin su dauki matakan da suka kamata wajen samar da zaman lafiya.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG