Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filayen Jiragen Saman Heathrow Da Gatwick Na Ingila Sun Samu Cikas


Heathrow
Heathrow

Yau an dakatar da tashi da saukar jirage a filayen Heathrow da Gatwick saboda matsalar na'urar kwamfuta

Manyan filayen jiragen sama biyu na London yau shake suke da dubban matafiya dake cikin bacin rai da takaici a sanadin lalacewar wasu na’urorin kwamfuta na filayen, abinda ya janyo aka soke tashin dukkan jiragen saman pasinja na British Airways.

A sanadin wannan al’amarin, yau dukkan jiragen da ya kamata su tashi daga filayen jiragen saman Heathrow da Gatwick an soke su.

Kamfanin British Airways dai bai fadi abinda ya janyo matsalar ba amma kuma ba wata alamar dake nuna cewa kutse aka yi.

Yanzu haka dai kamfanin na British Airways ya soma sanarda jama’ar dake da shirin tafiya da cewa kada suzo filayen jiragen nan Heathrow da Gatwick.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG