Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Binciki Yadda Aka Kwarmata Bayanan Sirri Kan Harin Birtaniya


Shugaba Donald Trump yace ya damu matuka da yadda ake kwarmatawa kafofin sadarwar Amurka bayanai akan binciken da ake gudanarwa na harin da aka kai a Manchester, ya kuma yi alkawarin gudanar da bincike.

Fallasa bayanan binciken da ake gudanarwa da ya hada da hotunan shaidun da ‘yan sanda suke da shi, ya harzuka masu gudanar da binciken Birtaniya. Ya kuma sa suka daina ba Amurka bayanan binciken da suke gudanarwa na dan lokaci jiya Alhamis.

"Na bukaci ma’aikatar sharia da sauran cibiyoyin da suka dace, su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamarin." Bisa ga cewar Trump a Brussels jiya alhamis. "Idan ta kama, a hukumta wanda yake da alhakin kwarmaton kamar yadda doka ta tanada."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG