Accessibility links

Firai Ministan kasar Habasha ya dauki hutun kula da lafiyarsa


Firai Ministan kasar Habasha Meles Zenawi

Hukumomin kasar Habasha sun ce Firai Ministan kasar Meles Zenawi zai dauki hutun kula da lafiyarshi

Hukumomin kasar Habasha sun ce Firai Ministan kasar Meles Zenawi zai dauki hutun kula da lafiyarshi, amma zai ci gaba da rike mulki yayinda yake jinyar cutar da ba a bayyana ba.

Kakakin gwamnati Bereket Simon ya yiwa manema labarai bayani a birnin Addis Ababa yau Alhamis bayan kafofin watsa labaran da aka yayata cewa, shugaban na Ethiopia yana kwance rai ga Allah a asibitin Saint Luc dake birnin Brussels na kasar Belgium.

Bereket ya musanta rahoton da ‘yan tawayen kasar Ethiopia suka buga a kan shafinsu na internet cewa Mr. Meles yana fama da sankaran kwakwalwa. Kakakin bai bayyana ciwon da Firai Ministan yake fama da shi ba, ko inda ake mashi jinya, sai dai yace “yana samun sauki” kuma har yanzu shine yake gudanar da harkokin mulki.

Wani kakakin gwamnati yace, likita ne ya ba Mr. Meles shawara ya dauki hutu, ya kuma ce zai koma bakin aiki da zarar ya sami sauki.

Tsohon jakaden Amurka a Ethiopia David Shinn ya shaidawa Muryar Amurka cewa, taron maneman labaran ya nuna cewa, rashin lafiyan “yana da tsanani.”

XS
SM
MD
LG