Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan kasar Thailand ya amince ya sha kaye a babban zaben da aka gudanar


Wata jami'ar gudanar da zabe tana nuna katin zabe yayin kirga kuri'a a birnin Bangkok, Thailand.

Firai Ministan kasar Thailand ya amince da kaye da ya sha a babban zaben da aka gudanar yau Lahadi, wanda jam’iyar adawa dake kawance da tsohon PM Thaksin Shinawatra da aka hambare ta lashe.

Firai Ministan kasar Thailand ya amince da kaye da ya sha a babban zaben da aka gudanar yau Lahadi, wanda jam’iyar adawa dake kawance da tsohon PM Thaksin Shinawatra da aka hambare ta lashe. Abhisit Vejjajiva ya taya abokiyar hamayyarshi Yingluck Shinawatra kanwar tsohon PM, wadda kuma ita ce shugabar jam’iyar Pheu Thai murna. Yingluck ce zata kasance PM mace ta farko a Thailand. Akasin harsashen da aka yi tun farko cewa za a yi tafiye keke-da-keke, jam’iyar Yingluck Shinawatra Pheu Thai ta sami gagarumin rinjaye a majalisa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG