Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan Togo Ya Yi Murabus


Firai Ministan Togo, Komi Sélom Klassou, Lomé, ranar 6 ga watan Maris, 2020. (VOA/Kayi Lawson)
Firai Ministan Togo, Komi Sélom Klassou, Lomé, ranar 6 ga watan Maris, 2020. (VOA/Kayi Lawson)

Fadar gwamnatin kasar Togo, ta ce Firai Ministan kasar da gwamnatinsa sun yi murabus daga mukamansu a cewra kamfanin dillancin labarai na AFP.

Shugaban kasar Paul Gnassingbe, ya mika godiya ga Firai Minista Komi Selom Klassou da tawagarsa, saboda irin kokarin da suka yi a fannin tattalin arziki da na siyasar kasar.

Shugaba ya kuma jinjina Masu musamman kan rawar da suka taka wajen yaki da annobar coronavirus da ta addabi duniya, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta na yanar gizmo ya nuna.

Tun tuni dai ya kamata a yi wa gwamnatin garanbawul, bayan da aka sake zaben shugaba Gnassingbe a watan Fabrairu domin yin wa’adi na hudu a ofis, amma kuma aka jinkirta yin sauyin sanadiyyar barkewar cutar ta COVID-19.

Nasarar da shugaban ya samu a zaben da aka yi, wacce ta biyo bayan sauya kudin tsarin mulkin kasar da aka yi, wanda ya ba shi damar sake tsayawa takara – ta sa danginsa samun damar ci gaba da zama akan karagar mulkin kasar har na tsawon sama da shekara 50.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG