Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Canada ya tabbatar kungiyar al-Qaida ta kashen dan kasar


Firayim Ministan Canada Justin Trudeau

Firaministan Canada Justin Trudeau, ya tabbatar da fille kan dan kasar tasu din nan John Ridsdel da aka yi garkuwa da shi a Kudancin Philippines a bara, bisa neman kudin fansa har Dalar Amurka Miliyan 21.

Wanda wasu ‘yan kungiya ta’addanci mai alaka da AlQaida suka nema. Kisan da Firaministan ya bayyana da cewa, ba wani dalilin yin kisan da ya wuce kisan gillar tsohon ma’aikacin da har ya yi ritaya.

Ridsdel na daya daga cikin ‘yan Canada din nan guda 2 da aka sace tare da wani manajan gandun daji dan kasar Norway a watan Disambar bara. Wanda makonnin biyu da sacesu ‘yan bindigar Abu Syyaf da wani suka fidda bidiyon neman kudin fansar.

Na neman Dala Miliyan 21 akan kowane mutum daya daga wadanda aka yi garkuwar dasu, sannan za a sake su. Inda aka ga wadanda aka sacen suna magiyar neman a ceci rayukansu a faifan bidiyon.

Bidiyon da ya bayyana a kwanan nan ya bayyana cewa za’a kashe Risdel a ranar 25 ga watan Afrilun nan idan ba a biya kudin fansar ba. Wannan sanarwa ta Trudeau ta fito ne bayan sanarwar ‘yan sanda.

Wacce ta bayyana cewa, wasu mahaya babura ne suka ajiye kan mamacin nade a leda kusa da wani ginin gwamnati. Har yanzu kuma babu labarin halin da sauran mutanen da aka sace ke ciki.

XS
SM
MD
LG