Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Isra'ila Ya Dakushe Duk Wata Fatar Tsagaita Wuta da Zirin Gaza


Benyamin Natanyahu Firayim Ministan Isra'ila
Benyamin Natanyahu Firayim Ministan Isra'ila

Jiya Litinin, Prime Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu ya dakushe duk wata fatar tsagaita bude wuta nan take a zirin Gaza, yana mai fadawa 'yan Isira'ila cewa suyi shirin fafatawa na lokaci mai tsawo da kungiyar Hamas.

Mr Netanyahu yayi wannan furucin ne ta gidan talibijin na kasar, a yayinda baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya bi sahun wasu shugabanin kasashe wajen yin kiran da'a tsagaita bude wuta nan take a Gaza. Ya zargi dukkan bangarorin da laifin rashin nuna halin dattako a rikicin na tsawon mako guda.

Bugu da kari kuma, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi kiran da'a tsagaita bude wuta na jin kai ba tare da gitta wasu sharudda ba. To amma Mr. Netanyahu yace kungiyar Hamas ce zata ci moriyar wannan shawara da aka gabatar, a yayinda shawarar zata yi watsi da bukatun matakan tsaron Isira'ila.

Ya zuwa yanzu dai wasu shugabanin kasashen duniya sun kasa sassauta rikicin daya kashe fiye da Palasdinawa dubu daya, yawancinsu farar hula da sojojin Isira'ila hamsin da biyar da kuma farar hular Isira'ila guda uku, tun ranar takwas ga wannan wata na Yuli.

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG