Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministar New Zealand Na Dab Da Zama Amarya


Firayim Ministar kasar New Zealand na dab da zama amarya bayan da saurayin da ya dade yana nemanta yayi mata tayin aure.

Firayim Minista Jacinda Ardern, da saurayinta Clarke Gayford sun bayyana shirinsu na yin aure a lokacin bikin Easter, a cewar mai magana da yawun Firayim Ministar.

Shi dai Gayford, wanda mai gabatarda wani shirin talabijin ne game da kamun kifi, shine mai kula da 'yar su mai wattani 10, da ya haifa tare da Firayim Ministar.

Da aka tambayi Firayim Minista Ardern a bara, idan ko ita ce zata yi wa Gayford tayin auren, sai tace a cikin raha, "Ina son in sanya shi zufa da jin jiki da wannan tambayar shi kansa, amma bazan kyale shi ba.”

Firayim Minista Ardern, mai shekaru 38, ita ce ta zama shugabar kasa ta biyu a duniya da ta taba haihuwa yayin da take kan karagar mulki.

Shugabar kasar Pakistan Benazir Bhutto, ita ce mace ta farko da ta haihu yayin da take shugabancin wata kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG