Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayin Ministan Kasar Spain Ya Gana Da 'Yan Majalissar Sa Akan Yankin Catalonia


Firayin Minista Mariano Rajoy na neman tabbaci daga shugabannin yankin Catalonia akan ko sun ayyana 'yancin kan yankin?

Yau Laraba Firayin Ministan kasar Spain Mariano Rajoy yace yana bukatar cikakken bayani daga shugabannin yankin Catalonia da bai da cikakken ‘yancin kansa akan ko sun ayyana samun ‘yancin gashin kai ko a’a.

Da yake magana bayan wata ganawa ta gaggawa da yayi da ‘yan majalissar kasar don tattauna gwagwarmayar da shugabannin yankin ke yi na ballewa, Rajoy ya ce akwai bukatar cikakken bayani daga kundin tsarin mulkin Spain wanda zai ba gwamnatinsa damar yin watsi da neman ‘yancin Catalonia.

Ganawar da suka yi yau Laraba na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban Catalonia Carles Puigdemont yayi wani jawabi mai nuna ayyana ‘yancin kai yayinda kuma yayi watsi da duk wasu matakan doka, a yanzu, don neman alfarmar ganawa da gwamnatin Spain.

Mai magana da yawun gwamnatin Rajoy ya ce babu yiwuwar wata ganawa tunda shugabannin Catalonia sun riga sun yanke shawarar suna so su balle.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG