Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yankin Catalonia na kasar Spain ya dan jingine ayyana yancin cin gashin kai


Shugaban yankin Catalonia na kasar Spain Carles Puigdemont
Shugaban yankin Catalonia na kasar Spain Carles Puigdemont

Shugabanin yankin Catalonia na kasar Spain sun dan sarara ga ayyana yancin cin gashin kai

Shugabanin yankin Catalonia na kasar Spain masu neman balewa sun dan sarara ga niyar su ta ayyana yancin cin gashin kai daga kasar Spain, ta hanyar dakatar da kaddamarwa da suka yi niyar har sai an gama yin shawarwari da gwamnatin Spain.

Shugaban yankin Catalonia, Carles Puihdemont ne yayi wannan furucin a jawabin da ya gabatarwa wakilan Majalisar yankin a yau Talata. Yayi kira ga gwamnatin Spain data yi shawarwari da su, kuma yace yankin Catalonia ya cancaci ayyana yancin cin gashi kai..

To amma mai magana da Prime Ministan Spain yace gwamnati bata yi na’am da ayyana yancin Catalonia ba, kuma gwamnati ba zata yi wani shawarwari ba, domin shugabanin Cataloia sun riga su yanke shawarar cewa suna son balewa

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG