Kafar yada labarai ta gwamnati a Sudan ta bayar da rahoton cewa Firai-Ministan kasar ya na cikin koshin lafiya, bayan an so a halaka shi a wani hari da aka kai mishi a yau Litinin.
Gidan talabijin na kasar ya ce Abdulla Hamdok yana kan hanyar sa ta zuwa ofis ne, lokacin da aka kai wa ayarin motocinsa hari da Bom a Khartoum babban birnin kasar.
Babu wani dai da ya dauki alhakin harin.
Hamdok, dai ya zama Firai Ministan kasar ne a watan Augusta bayan da aka cire shugaba Omar Al-Bashir mai mulkin kama karya, bayan zanga-zanga da aka sha yi a fadin kasar ta nuna adawa da gwamnatinsa.
Ana dai tsare da Bashir a gidan kurkuku na Kober, inda ake tsare da mafi akasarin masu adawa da shi, kuma aka gana musu azaba.
Gwamnatin Sudan ta ce zata mika Al-Bashir ga kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya, don gurfanar da shi.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 06, 2023
NIJAR: Yawan Matan Da Ke Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu.