Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Mutum Miliyan 6 Ke Dauke Da Covid-19 a Amurka


Yadda aka shiga da wani cikin motar daukar mara sa lafiya

Yawan masu dauke da cutar corona a Amurka ya zarce miliyan 6, baya ga yawan mace-mace dubu 183, wanda ya zarce na kowace kasa a duniya.

Kwanan nan wasu jihohi hudu na yankin tsakiyar yammacin kasar, su ka bada rahoton adadin sabbin kamuwa da cutar a rana guda, irin wanda ba su taba gani ba.

Jihar Iowa 785, jihar North Dakota 375, Jihar South Dakota 425 sannan jihar Minnesota 1000, bisa ga alkaluman Jami’ar Johns Hopkins.

Lokacin da ake yi wa wani gwanin Cutar Coronavirus
Lokacin da ake yi wa wani gwanin Cutar Coronavirus

A halin da ake ciki kuma, jihohin Montana da Idaho sun ce yawan wadanda tsananin ciwonsu na COVID-19 ya kai ga sai an kwantar da su, na matukar karuwa.

A yayin da yankin tsakiyar yammacin kasar ya kasance na baya-bayan nan wajen ganin yawan masu kamuwa da cutar, a kasar gaba daya, yawan mace mace da kwanciya a asibiti, da kuma kamuwa da cutar, na ta raguwa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG