Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayi Ministar Kasar New Zealand Ta Haifi 'Ya Mace.

Fira-Ministar Kasar New Zealand Jacinda Ardern Tare Da Mijinta Clark Gayford Da Kuma Diyar Da Suka Haifa.
Fira-Ministar Kasar New Zealand Jacinda Ardern Tare Da Mijinta Clark Gayford Da Kuma Diyar Da Suka Haifa.

Fira-Ministar New Zealand din Jacinda Ardern, ta manna hoton diyar da ta haifa a shafinta na Instagram yau Alhamis, tare da mahaifin 'yar Clark Gayford.

Fira-Ministar New Zealand din Jacinda Ardern, ta manna hoton diyar da ta haifa a shafinta na Instagram yau Alhamis, tare da mahaifin 'yar Clark Gayford.

Ta ce har yanzu dai bata radawa diyarta suna ba, amma ta haifeta cikin koshin lafiya kuma tana da nauyin kilo 3 da digo 31.

Ardern 'yar shekaru 37 ce, kuma ita ce Fira-Ministar mace ta uku data sami wannan mukami a tarihin New Zealand, sannan tana cikin shugabannin kasashen duniya mata kalilan da suka haihu yayin da suke kan karagar mulki.

Cikin wadanda suka haihun akan mulki mata, har da ta karshe kasgin ita, ita ce tsohuwar Fira-Ministar kasar Pakistan wato Benazir Bhutto, tun a shekarar 1990. Sai kuma yanzu da aka sami ita Jacinda ta haihu lokaci da take kan karagar mulkin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG