Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fulani Na Kokawa Da Rashin Kulawa Da Lafiyar Dabbobinsu


Wani Makiyayi da Shanun Shi.

Makiyaya a Jahar Filato na matukar korafi kan rashin shawo kan bullar sabuwar cutar dabbobi

Wakiliyar Sashin Hausa Zainab Babaji ta bada rohoton cewa “al’umar Fulani sun koka matuka akan bullar wata cuta da ke shafar huhun dabbobi kuma lamarin yayi sanadiyyar mutuwar dubban shanu a Najeriya”.

Sakataren kungiyar miyatti Allah “cattle breeders” na jahar Nasarawan Najeriya wato Mohammadu Hussaini yace “cibiyar samar da rigakafi da magungunan dabbbobi da ke VOM a jahar Filato ce keda alhakin samar masu da magungunan.

Amma a halin da ake ciki yanzu shine makiyayan na ketarawa zuwa kasar kamaru ne kafin su samo wannan magani a cewar sakataren kungiyar, kuma hakan ya sa Fulani da dama asarar dabbobinsu, “ya ce fiye da shanu dubu uku su ka mutu cikin dan kankanin lokaci”.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG