Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni Sun Tsere Sakamakon Sakacin Jami'ai A Filato


Yunkurin Fasa Gidan Yari A Bauchi

An kafa kwamitin bincike akan mataimakin shugaba da jami'an hukumar gyara hali ta Najeriya a jihar Filato, sakamakon tserewa da wasu fursunoni suka yi daga babban gidan yari da ke jihar.

Hukumar gyara hali ta Najeriya a jihar Filato ta tabbatar da cewa mutum hudu da ake tsare da su wadanda ake tuhuma da laifin fashi da makami da kuma satar mutane sun yi layar zana daga gidan kaso na hukumar da ke jihar.

Shugaban hukumar na jihar Filato Mista Samuel Aguda ne ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya bayyana hakan a matsayin sakaci daga ma’aikatan dake bakin aiki a lokacin da lamarin ya faru.

Agudu ya kuma ce duk ma’aikaci ko jami’in da aka kama da hannu a ciki zai fuskanci hukunci.

Mista Aguda yace ana gudanar da binciken kan mataimakin kontrolan hukumar mai kula da ayyukan hukumar a jihar don gano yadda lamarin ya auku.

Ya kara da cewa tuni aka kafa wani kwamitin masu bincike na musamman a tashoshin mota, kasuwanni da sauran wurare domin sake cafke fursunonin da suka arce.

Aguda ya bada tabbaci ga jama’a cewa za’a kamo fursunonin nan ba da jimawa ba, ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar jijar da su taimaka da duk wasu bayanai da za su kai ga sake damke fursunonin.

XS
SM
MD
LG