Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

G5 SAHEL: Za Mu Kawar Da 'Yan Ta'adda A Yankin Mu


Taron Shuwagabannin G5 Sahel
Taron Shuwagabannin G5 Sahel

Shugabannin kasashen G5 Sahel sun gudanar da wani taron gaggawa a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar da nufin daukan matakan magance hare haren 'yan ta'adda a yankin.

A makon da ya gabata wadansu mahara da ba’a san ko su waye ba sun kai wani mummunan harin da ya hallaka sojojin jamhuriyar Nijar sama da 70 a barikin sojan Inates da ke kan iyakar Mali da Nijar.

Wannan wata alama ce da ke nuni da cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel sun fara gawurta, inda kasashen yankin tuni su ka fara daukan matakan murkushe su.

Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya ce ‘yan ta’adda sun fara fadada hare haren su zuwa wurare da dama, inda suke amfani da manyan makamai yaki suna afkawa jami’an tsaro tare da nuna kiyayya ga sojojin kawance masu sansani a yankin Sahel.

“Ya kamata wadanda suke wannan aiki cikin sani ko rashin sa da masu sukar kawancenmu da kuma wadanda suke ganin ya kamata a rushe wannan tafiya su sani yin hakan yafi kaiwa dakarunmu hari muni,” a cewar shugaba Issouhou.

A lokacin da yake karanta sanarwar karshen taron shugabannin kasashen G5 Sahel, Ministan Harkokin Wajan Nijar, Kalla Hanlourau, ya yi kira da kasashen duniya da su taikamaka ma su, yayin da kasashen suka kuduri aniyar kaddamar da wani farmaki da aka yiwa lakabi da “Operation Takobi” akan iyakokin Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.

Kasashen na yankin Sahel sun kuma yi alkawarin daukan Matakan kawo karshen wasu haramtattun sana’o’i da ake yi kamar safarar makamai da miyagun kwayoyi da dai sauransu, saboda suna taimakawa ‘yan ta’adda samun kudaden shiga.

Bayan kammala taron nasu shuwagabannin kasashen yankin Sahel a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar sun kai ziyarar girmamawa a inda aka binne sojojin Nijar 71 da suka rasa rayukansu a harin da aka kai musu a barikin sojan Inates.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG