Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gadaje Sun Kare a Sashen 'Yan Gobe Da Nisa a Asibitocin Florida


Wasu masu jinya a wani asibiti da ke kasar Italiya

Rahotanni daga Amurka na nuni da cewa wasu jihohin kasar na fuskantar matsalar wuraren jinyar masu fama da cutar COVID-19 yayin da adadinsu ke karuwa.

Asibitoci 45 a jihar Florida da ke kudancin Amurka sun ba da rahoton cewa gadaje sun kare a sashen da ake kula da marasa lafiyan da jikinsu ya yi tsanani.

Hakan na faruwa ne yayin da yaduwar cutar coronavirus ke ci gaba da durkusar da fannin kiwon lafiyar kasar.

Jihar ta Florida, ta ba da rahoton samun karin sama da mutum dubu 12,000 da suka kamu da cutar a jiya Lahadi, rana ta biyar kenan a jere da jihar ke ba da rahoton samun sama da mutum dubu 10 da cutar ta harba a yini daya.

Wasu likitoci a lokacin da suke kula da wani mai jinya
Wasu likitoci a lokacin da suke kula da wani mai jinya

Yankin Miami ya kasance wanda yaduwar cutar ta fi tsanani, inda anan ne tara da daga cikin asibitoci 45 da gadajensu suka kare suke.

A yau Litinin dokar cin tara akan duk wanda ya ki saka takunkumin rufe baki da hanci da Magajin Gari Francis Suarez ya saka za ta fara aiki, inda za a ci tarar duk wanda ya karya dokar a karon dala 50 sannan a ci tarar duk wanda ya sake karya dokar dala 500.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG