Gwamnatin Jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya, ta ba Sarki Muhammadu Sanusi II wa’adin kwana biyu domin ya bayyana matsayarsa kan mukamin shugaban Majalisar Sarakunan jihar da aka nada shi.
Wata wasika da fadar gwamnatin jihar ta aika wa Sarki Sanusi a yau Juma’a kamar yadda rahotanni suka nuna a Najeriya, ta nemi Sarkin da ya ba da amsar amincewa da mukamin ko akasin haka cikin kwana biyu.
Wasikar ta samu sa hannun Sakataren fannin kula da ayyuka na musamman a jihar, Musa Bichi kamar jaridar yanar gizo ta Premium Times ta ruwaito.
A baya-bayan nan, gwamantin ta jihar Kano, ta nada Sarki Sanusi a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.
Cikin wasikar, an umurci Sarki Sanusi, da ya kira taron kaddamar da majalisar ba da bata lokaci ba, kamar yadda doka ta tanada.
Gidan talbijin na Channels a Najeriya, ya ruwaito Ganduje yana cewa, “ya na da muhimmanci Sarki Sanusi ya bayyana matsayar amincewa da mukamin ko akasin hakan.”
Ita dai gwamnatin jihar ta Kano ta bayyana cewa, za a rika karba-karba ne kan mukamin shugaban majalisar a tsakanin sarakunan jihar masu daraja ta daya.
A idon mutane da dama, kamar yadda Muryar Amurka ta lura, wannan mataki na bai wa fadar wa’adin kwana biyu ta bayyana matsayarta, ci gaba ne na takaddamar kirkiro masarautu hudu da gwamanti ta yi a baya.
Jama’a da dama na kallon matakin kirkirar masarautun a matsayin wata dabara ta rage karfin ikon Sarki Sanusi, wanda rahotanni ke nuni da cewa yana yawan sukar lamirin gwamnatin Gwamna Ganduje.