Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yi Wani Kasaitaccen Gangami Anan Washington DC Asabar Din Nan


Gungun jama'a da suka halarci gangamin na farko shekaru 20 da suka wuce.

Wannan shine cikar shekaru 20 da aka gudanar da irin wannan gangami na farko a 1995.

Ana sa ran dubban mutane ne zasu hallara anan birninn Washington DC a karshen wannan mako domin tunawa da cikar shekaru 20 da ayyana wani gangamin bakar fata da aka lakabawa sunan "Macin mutane Milyan daya".

A shekarar 1995 ne shugaban wata kungiyar musulmi bakar fata ta Amurka da ake kira "Nation of Islam" Louis Farrakhan, ya gayaci bakar fatan Amurka maza su hallara a Washington inda zasu yi alkawarin zasu kyautata hallayarsu a zaman magidanta, ko iyaye ko shugabannin al'uma.

Gangamin shine na hudu mafi girma a tarihin gangami a nan birnin Washington, kuma mafi girma inda bakar fata zalla suka hallara.

Amma a bana an gayyaci maza da mata daga ko wani jinsi ko addini su halarci gangamin da za'a yi Asabar din nan mai taken "A yi Adalci ko kuma".

Burin gangamin na bana inji wadanda suka shirya taron, shine a karfafa kiraye kirayen neman adalci bayan harbe harben da aka yiwa bakar fata har lahira da ake zargi kan jami'an tsaro. Abunda za'a maida hankali a bikin zagayowar wannan rana.

An maida hankali kan irin dangantakar da take akwai tsakanin bakar fatar Amurka da 'Yansanda tun bayan bindige matasa bakar fata Trayvon Martin, da wani mai aikin gadi yayi a shekara ta 2012 a Florida, da kuma Michael Brown, a lokacin wani tashin hankali tsakaninsa da wani dansanda a Ferguson Missouri. Tun bayan haka mutuwar wasu bakar fata a hanun "Yansanda ya janyo zanga zanga karkashin wata laimar da ake kira Black Lives Mattars" da turanci, watau ran bakar fata ma yana da tasiri ko muhimmanci".

Ana sa rana shugaban kungiyar ta Nation of Islam Louis Farrakan, zai yi jawabin a zaman babban bako da misalin karfe daya na rana agogon Washington DC.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG