Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Garin Chibok Da Mutanensa Abin Tausayi Ne


Wata Uwa Na Kukan Rshin 'Yan Chibok

Har yanzu masu fafutuka irinsu Dakta Obiageli Ezekwesili da IG Wala na ci gaba da kira kan 'yan matan Chibok da shi kansi makomar garin nasu, wanda ya bayyana a matsayin abin a tausaya musu ne.

Shugabar kungiyar rajin kiran ceto daliban Chibok Dakta Obiageli Ezekwesili ta furta cewa dole su ci gaba da gwagwarmaya ya hanyar nunawa gwamnati kurakurai da zarar sun gano su. Saboda haka suna kan bakan sun a bin diddikin ganin an sako ‘yan matan nan na garin Chibok da aka sace tun kwanaki 594 da suka shude.

Tun wancan lokaci ne tawagar masu rajin ganin an dawo da ‘yan matan suka kafa kahon zukar tarurruka da zanaga-zangar lumana daban-daban don ganin haka ta cimma ruwa, amma sai gashi shekaru biyu na nema haduwa ba tare da jin duriyarsu ba.

Asali ma dai mutane da yawa suna has ashen kila ‘yan matan nan kanana da ake amfani da wasun su wajen tayar da bama baman kunar bakin wake ta yiwu wasun su ne ake tursasawa ko kuma aka juya tunaninsu suka rikide.

Shima wani dan rajin kare hakkin matasa Kwamrade Ibrahim Garba Wala cewa yayi Allah ne kadai yasa yadda zata kaya game da ceto ‘yan matan na Chibok. domin kuwa ko sojojin da ke bakin daga yace ba zaka ji suna cewa ga ranar da za su gano yaran ba.

IG Wala ya bayyana yadda suka ga garin Chibok ya zama abin tausayi musamman yadda mutane suke a takure a dalilan harkokin sintiri masu alaka da tsaro a yankin. Shima Kanar Rabe Abubakar daraktan yada labaran rundunar tsaro sojojin yace, daga ‘yan matan Chibok har ma wadanda bas u ba da aka yi garkuwa dasu yana sa ran da sannu za su ceto su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG