Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: APC Ta Nemi a Bata Kujerar Gwamnanta


A man dressed as Santa Claus visits and gives Christmas presents at a family's home on the Christmas Eve in Espoo, Finland.

Biyo bayan soke zaben gwamnan Taraba na PDP da kotun sauraran karaarrakin zabe tayi kimanin kwanaki 21 da suka gabata jam'iyyar APC ta nemi gwamnan ya bata kujerarta saboda wai bai daukaka kara ba cikin kwanaki 21 kamar yadda doka ta tanada

Yanzu jam'iyyar APC tana cewa a bata kujerarta domin katun zabe ta riga ta rushe zaben gwmna Darius Isyaku na jam'iyyar PDP.

APC ta bakin shugabanta na jihar Alhaji Alhassan Jika Ardo tace har lokacin da wa'adin daukaka kara ke cika bata samu takardar cewa gwamnan ya daukaka kara ba. Saboda haka a bata kujerarta kamar yadda doka ta shimfida.

Amma a martanin da ya mayar gwamnan jihar Darius Isyaku ya musanta batun cewa bai daukaka kara ba.Ta bakin hadiminsa Alhaji Abubakar Bawa yace ba dole ne sai sun sanarda jam'iyyar APC ba. Idan suna son su sani su je kotu su tambaya.

Shugaban kungiyar lauyoyi a Jalingo fadar jihar Barrister Idris Abdullahi Jalo yace idan sun daukaka kara cikin kwanaki 21 ya rage ga kotu ta sanarda ita APC. Hurumiin kotu ne ta sanarda duk wadanda karar ta shafa.

G karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG