Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Black Stars Ta Ci Angola 1-0 Da Kyar A Kumasi


Ghana Black Stars Line-up
Ghana Black Stars Line-up

Dan wasan gaba na kungiyar Bournemouth, Antoine Semenyo ne ya zura kwallo daya tilo a wasan inda Black Stars ta Ghana ta doke Palancas Negras ta kasar Angola a filin wasa na Baba Yara.

Dan wasan da ya shigo bayan hutun rabin lokaci shine ya girgiza raga daga bugun tazara na kusan karshen wasan da ya baiwa bangaren Chris Hughton nasara a wasansa na farko matsayin kocin Black Stars.

Ghana Black Stars Bench
Ghana Black Stars Bench

Nasarar ta sa Ghana ta zama ta daya a rukunin E bayan ta samu maki bakwai a wasanni uku da Angola da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da dukaninsu ke da maki hudu hudu.

Mohammed Kudus ne ya fara samun dama ta farko a Black Stars amma dan wasan tsakiyar na Ajax ya kasa zura kwallo inda ya daga kwallo ta yi sama sosai bata yi kusa da raga ba.

Mohammed Kudus
Mohammed Kudus

Dan wasan Angola Gelson Dala ya tilastawa Golan Ghana Lawrence Ati-Zigi yin tsalle ya buge yayin da ya aiko da kwallo a kusa da akwatin Ghana.

‘Yan wasan Angola sun hana Kudus zura kwallo ne a mintuna na 18 da 27, inda golan Angola, Neblu, ya kara kaimi.

Ghana and Angola in action
Ghana and Angola in action

Yayin da Black Stars suka samu damarmaki a farkon rabin wasan, sun gaza kada raga inda zagayen farko ya kare wanda babu ci kwallo.

Ko a zagaye na biyu wasan bai yi wa Ghana kyau ba yayin da bangaren Hughton ke fafutukar ganin ta doke abokan karawan su dake suka bakwanci Kumasi.

Ghana Black Stars in action
Ghana Black Stars in action

Sai dai kuma saura minti daya a tashi daga wasan, Semenyo ya mayar da martani da sauri ga kwallon da ta fado gabansa a cikin akwatin 18, inda ya zura kwallon da ta baiwa Ghana nasarar da take bukata.

Yanzu dai ‘yan wasan Black Stars za su maida hankali a wasansu na gaba a ranar Litinin 27 ga Maris, lokacin da za su je birnin Luanda don karawa da Angola.

-Hotuna daga Hukumar GFA

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG