Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Gwamnati ta Haramta Yin Anfani da Leda


Abun da ambaliyar ruwa ya jawo a Accra Ghana

Shugaban kasar Ghana yace leda ta cika tekunan kasar wadda kuma ita ce ta yi sanadiyar ambaliyar ruwan da ya lakume rayuka da dukiyoyi da dama kwanakin baya.

Shugaba John Dramani Mahaman yace wajibi ne su fito da hanya mai kyau na kawar da sharar leda.

Yace idan basu iya fito da wata hanyar sharar leda ba to ko zasu haramta anfani da ita.

Kafin kashedin na shugaban mataimakinsa Kwasi Atta ya kira a yi muhawara akan haramta yin anfani da leda saboda shararta ce tayi sanadiyar mummunan ambaliyar ruwan sama ta ranar uku ga watan Yuni wacce tayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da asarar dimbin kadarori da aka yi abirnin Accra.

Mataimakin yace zagawa da yayi a wasu wurare da dama sharar leda ce ta cike butoci da tafkoki wanda ahalin yanzu ana yasheta a manyan tafkokin birnin Accra guda biyu.

Sharar leda dai na cigaba da zama barazana ga kasar. Kazalika ledar tana gurbata kasar shuka tare da yiwa dabbobi illa muddin suka ci leda.

A can arewacin kasar jama'a na kokawa akan sharar leda. Su ma nasu dabbobib na mutuwa idan suka hadiyeta. Sharar leda ta maimaye koina da ina maimakon su mayarda hankali akan ayyukansu.

Amma kungiyar ma'aikatan kayautata muhalli cewa tayi haramta yin anfani da leda ba ita ba ce mafita sai dai a bullo da hanyoyin tattalin sharar ledan. Yin hakan ne kawai zai taimaka.

Shugaban kungiyar yace akwai mutane masu shigowa da leda iri iri kuma babu ruwansu da shararta. Yace idan aka dora masu haraji kuma aka rage sha'awar anfani da leda za'a cimma manufa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG