Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Jam'iyyar NPP Mai Mulki Ta Zabi Dr. Bawumia A Matsayin Dan Takaran Shugaban Kasa


TARON NPP
TARON NPP

Jam'iyyar NPP mai mulki a Ghana ta zabi mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a babban zaben 2024, inda zai fafata da tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama na babbar jam’iyar adawa ta NDC da wasu ‘yan takaran.

Dakta Bawumia ya kasance mutum na farko daga yankin arewacin Ghana da zai jagoranci jam'iyyar ta NPP a matsayin dan takaran shugaban kasa.

Mataimakin kwamishinan hukumar zabe ta kasa, Dakta Serebour Quaicoe shi ne ya sanar da sakamakon zaben. Yace: “Dokta Bawumia ya samu kuri'u 118,210 wato kashi 61.47%; yayin da dan takara mafi kusa da shi, Kennedy Agyapong, ya samu kuri'u 71,996, wato kashi 37.41%; Dakta Afriyie Akoto, wanda ya zo na uku, ya samu kuri'u 1,459, wato kashi 0.76%; sai Addai-Nimoh ya samu kuri'u 731, daidai da kashi 0.41%. Don haka, an zabi Dakta Mahamudu Bawumia a matsayin dan takarar jam'iyyar da zai tsaya takara a 2024.

TARON NPP
TARON NPP

Da yake jawabi ga dubban magoya baya, bayan sauran abokan takararsa sun yi jawaban mubaya’a gare shi, a wajen wani gangami da aka shirya a filin wasa na Accra, domin kaddamar da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar NPP, Dakta Bawumia ya ce an samu shakku kan nasarar da ya samu sakamakon zazzafar farfagandar da ake yi wa jam’iyyar NPP da cewa na kabilanci ne, inda ya jaddada nasarar da ya samu cewa za ta kau da wannan farfagandar.

Wasu manazarta sun nuna shakku kan samun damata, wasu kuma kai tsaye suka yi watsi da yiwuwar jam’iyyar NPP za ta zabi dan takara daga yankin Arewacin kasar nan. A fili sun yi kuskuren fahimtar ra'ayin jam'iyyar ta mazan jiya da nufin kabilanci ko bangaranci.”

TARON NPP
TARON NPP

Dakta Bawumia ya kara da cewa: “Ga maza da mata na mu na Zongo da ke warwatse a yankuna 16 na Ghana, ina gaya muku cewa a cikin jam'iyyar NPP, za a iya hawa sama. Ina gayyatar ku da ku kasance tare da mu a cikin wannan tafiya mai yiwuwa. NPP tana da wurin ku.

Wasu magoya bayan jam’iyar sun bayyanawa Muryar Amurka murnarsu, musamman da dan takaran ya kasance Musulmi kuma dan Arewa.

TARON NPP
TARON NPP

Alhaji Abdul Aziz Haruna Futa shi ne shugaban kungiyar Nasara ta Jami'iyar, wato mukamin dake kula da al’amuran ‘yan Zango da Arewacin Ghana na jam’iyar, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa, yana murna ne kwarai domin jam’iyarsu ta NPP bata taba zaben Musulmi kuma dan Arewa a matsayin dan takara ba sai wannan karon, kuma yana ganin zai kayar da tsohon shugaban kasa, John Mahama a zabe na gaba, domin: “Ya fi duk wadanda suka yi takara da shi ilimi, har da John Mahama. Ya san kan aiki (shugabanci); kuma shi kadai ne zai iya canja Ghana.”

Wata daga cikin mogoya bayan jam’iyar ta ce: “Bawumia ne zai iya kai mu ga nasara; shi ne zai iya sa mu ‘Break The 8’ (wato, zarce ala'adar shekru 8 ko wa'adi biyu da manyan jami'iyu kasar biyu suke yi a karagar mulki tun farko jamhuriya ta biyu)

Shugaban kasa, Nana Akufo-Addo, a dan gajeren jawabin da ya yi, ya bayyana kwarin gwuiwarsa kan Dakta Bawumia cewa zai iya hada kan jam’iyyar, tare da taimakon sauran ‘yan takara uku, domin samun nasara kan John Mahama na jam’iyar NDC a zaben 2024.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG