Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Ra'a'yoyin Masharhanta Kan Takunkumin ECOWAS Ga Kasar Nijar


Taron Kungiyar ECOWAS
Taron Kungiyar ECOWAS

Bayan kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma (ECOWAS) ta kakaba takunkumi ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Nijar, wasu mashaharta a kasar Ghana sun bayyana ra’ayinsu game da matakin da ECOWAS ta dauka kan kasar Nijar.

Mashahartan suka ce matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan sojojin da suka yi juyin mulkin ya yi daidai, domin hakan zai zama izna ga wasu da ke da burin yin juyin mulki a nan gaba. Rashin daukar tsattsauran matakin kan kasashen Mali, Burkina Faso da Guinea da suka yi juyin mulki a baya baya nan ya taimaka wajen wannan juyin mulkin, in ji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Yunus Swalahudeen Wakpenjo.

Baya ga takunkumin ECOWAS, kasar Faransa da ta yi wa Nijar mulkin mallaka, ta yi Allah wadai da juyin mulkin. Kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da hadin gwiwar tsaro da taimakon kudi ga Nijar, yayin da Amurka ta yi gargadin cewa taimakon da take bayarwa ga kasar na cikin hadari.

Saurari rahoton Idris Abdullah a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG