Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Ce Burkina Faso Ta Dau Hayar Sojojin Rasha Ta Biya Su Da Wurin Hakar Ma’adanai

Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo (AP)
Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo (AP)

Don haka kasar ta Ghana na ce sa sojojin hayar aiki a kan iyakarsu ta arewaci yana da matukar damuwa a gare ta.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce gwamantin mulkin sojan Burkina Faso ta dauki hayar sojoji daga Rasha don su taimaka wajen yaki da masu tayar da kayar baya a kasarsu, kuma suna amfani da wurin hakar ma’adanai domin biyansu.

Masu da’awar kishin Islama sun kara kutsawa cikin kasar Burkina Faso, lamarin da ya haifar da juyin mulki sau biyu a wannan shekarar: daya a watan Janairu, daya kuma a watan Satumba, a daidai lokacin da sojoji ke kokarin maido da mulki a kasar.

Masana sun yi imanin cewa shugaban Burkina Faso na yanzu, kyaftin Ibrahim Traore, yana amfani da sojojin hayar Rasha daga kamfanin Wagner don yakar masu ikirarin jihadi.

Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo A Babban Taron Shugabannin Amurka Da Afirka A Washington D.C.
Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo A Babban Taron Shugabannin Amurka Da Afirka A Washington D.C.

Da yake magana a ranar Laraba a Washington a wani bangare na babban taron shugabannin Amurka da Afirka, shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya bayyana damuwarsa game da wannan al'amarin da ake zargin ya auku.

Ya ce “A yau, sojojin haya na Rasha suna kan iyakarmu ta arewa. Yanzu haka Burkina Faso ta shiga wani shiri na tafiya tare da Mali wajen daukar sojojin Wagner aiki a can, kuma na yi imanin cewa an ware musu wani wurin hakar ma’adanai a kudancin Burkina Faso aka basu a matsayi wani nau’i na biyan kudin aikinsu. Sa su aiki a kan iyakarmu ta arewaci yana da matukar damuwa a gare mu a Ghana.”

​
XS
SM
MD
LG