Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar Kudi Ta Duniya Na Neman Dala Biliyan $15 Domin Yaki Da Manyan Cututtuka


Global Fund

Gidauniyar tallafin kudin yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da kuma zazzabinr cizon sauro, tace tana bukatar dala biliyan goma sha biyar domin kauda wadanan cututtuka.

Gidauniyar tallafin kudin yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da kuma zazzabinr cizon sauro, tace tana bukatar dala biliyan goma sha biyar domin kauda wadanan cututtuka.

A ruhoton da kungiyar ta fitar, tace kudaden da ake bukata zasu iya taimakawa wajen jinyar cututukan idan ba haka ba kuwa zai zama dole a kashe sama da dala biliyan $47 nan gaba wajen jinyar masu fama da cuturtukan. Kashe biliyan goma sha biyar yanzu a yaki da cututkan kuma hukumar tace zai taimaka wajen ceton rayukan miliyoyin mutane. Sai dai gidauniyar tayi gargadin aiki da cewa idan aka makara za a rasa wannan damar.

A cikin hirarta da manema labarai, wata babbar jami’a a fannin harkokin bincike wadda kuma ta taba zama member hukumar darektocin gidauniya Joanne Carter, ta gayawa ‘yan jarida cewa rashin yin komai yafi yin wani abu domin kauda wadanan cututukar muni. Ta kuma bayyana cewa, an kai matsayin da dole a yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro. Bisa ga cewarta, idan aka tara kudi sosai yanzu za a iya ceton miliyoyin rayuka da kuma iya kauda wadannan cututtuka.

Gidauniyar dake da shelkwata a Geneva ce take tara kimanin kashi daya bisa hudu na kudaden da aka kashewa a yaki da kanjamau, da kuma yaki da tarin fuka da zazzabin cizon sauro. Kungiyar da aka kafa a shekara ta dubu biyu da biyu, tana tara kudade bayan kowanne shekaru uku, ta kuma tara sama da dala biliyan goma sha biyu a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu domin yaki da cututukan a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Bisa ga cewar hukumar lafiya ta duniya, kimanin mutane miliyan dari biyu da goma sha tara suka kamu da zazzabin cizon sauro a shekara ta dubu biyu da goma, ya kashe mutane dari shida da sittin daga ciki. Haka kuma mutane miliyan talatin da hudu suke dauke da kwayar cutar HIV a karshen shekara ta dubu biyu da goma sha daya, Yayinda mutane miliyan daya da dubu dari bakwai suka mutu a shekarar, ya ragu daga mutane miliyan biyu da dubu dari uku da suka mutu a shekara ta dubu biyu da biyar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG