Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar Sardauna Ta Mayarda Hankali Akan Zaman Lafiya da Fahimtar Juna


Late Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto kuma Firimiyan Farko na Arewa

Shugaban kungiyar tuntuba ta Arewa ko ACF Alhaji Ibrahim Kumasi yace kungiyar na kokarin ganin ta tattauna da takwarorinta na kudanci da yammacin Najeriya domin samun masalaha daga tashe-tashen hankula da ake samu

Alhaji Kumasi yace sai an fahimci juna da hadin kai kafin a samu cigaba a kasar.

Yace zaman lafiya da fahimtar juna su ne abun da Gidauniyar Sardauna ta tasa gaba.Yace suna son su tattauna da shugabannin kabilar Igbo da na Yarbawa. Suna son su san abun da za'a yi a dakile rigingimun dake faruwa. Suna neman zaman lafiya da fahimtar juna da cigaba.

Kungiyar ta yi tunanen hada gwamnonin arewacin Najeriya domin a samu cigaba da cudanya da juna. Saboda haka zasu fadakar da sabbin gwamnoni akan abun da suke yi kuma su cigaba da taimakawa kungiyar.

Tsohon gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu shi ya yiwa manema labarai karin haske game da taron gidauniyar. Sun taru su duba abubuwan da gidauniyar ta dinga yi tun lokacin da aka kafata. Sun tabbatar cewa idan babu hadin kai cigaba zai yi wuya. Suna son su tabbatar sun zauna lafiya cikin lumana da walwala. Saboda haka ne yawancin dattawan arewa suka kasance a wurin taron.

Amma tsohon ministan ilimi Malam Ibrahim Shekarau cewa ya yi akwai bukatar samar ma matasa ayyukan yi tare da fadakar dasu akan babban kalubale dake gabansu.. Yakamata su fahimci ma'anar rayuwa da mahimmancin samun abun yi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG