Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Mai Karfin Awo 8 Da Digo 6 Ta Jijjiga Kasar Indonesia


Mutane na kokarin gujewa girgizar kasar a Banda Aceh

Girgizar kasar ta sa an yi jan hankali game da afkuwar tsunami a wasu garuruwa

Hukumar binciken yanayin karkashin kasa ta Amurka (USGS a takaice) ta ce wata girgizar kasa mai karfin 8.6 a ma’aunin girgizar kasa, ta jijjiga gabar arewa maso yammacin Indonesia, wanda ya janyo barazanar ambaliyar tsunami a fadin tekun Indiya.

Girgizar kasar ta shafi wani yanki mai nisan tazarar kilomita 430 a Kudu maso yammacin Banda Aceh, hedikwatar lardin Aceh kuma birni mafi girma a lardin, ya kuma kai zurfin kimanin kilomita 22. Kuma bayan kimanin sa’o’i 2 da faruwar girgizar kasar, Hukumar ta USGS ta bayar da rahoton aukuwar hucin girgizar kasar mai karfin 8.2 a ma’aunin girgizar kasa.

A shekara ta 2004, wata babbar girgizar kasa mai karfin 9.1 a ma’aunin girgizar kasa kusan a wannan wurin na tsibirin Sumatra da ke Indonesia, ya haifar da tsunami a Tekun Indiya wanda ya hallaka kimanin mutane 230,000 wadanda kusan rabinsu a lardin Aceh su ke.

Girgizar kasar ta yau Laraba ta faru ne da zurfi iri daya da ta 2004 ta Tekun Indiya. Rahotanni sun ce ta girgiza gine-gine har zuwa can Singapore, da Thailand da Indiya.

Cibiyar Gargadin Ambaliyar Tsunami ta Pacific ta bayar da gargadin yiwuwar Tsunami ga kasashe da yankunan da ke iyaka da Tekun Indiya. A sa’ilinda cibiyar ta ce ta gano igiyar ruwa mai doron santimita 30 a kusa da Aceh, ta ce mai yiwuwa dai babbar tsunami ta huce kan wasu gabobin ruwan.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG